Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto "Neven Mimica" shugaban hukumar raya kasashen da tallafawa kasashen duniya na tarayyar Turai yana fadar haka a ranar Alhamis da ta gabata, kuma ya kara da cewa sun bada kudaden ne don tallafawa kasar Gambia ta farfado daga mummunan halin da take ciki na tattalin arzikin kasar.
Wannan taimakon dai yana zuwa ne makonni kadan daga hawan kan kujerar shugabancin kasar ta Gambiya wanda Adama Barrow yayi. Hukumar ta kara da cewa za'a kashe wadannan kudade ne a fagagen tsaro, raya tattalin arziki da samarwa mutanen kasar ayyukan yi da kuma gina hanyoyi.
Kafin haka dai kungiyar tarayyar ta Turai ta dakatar da tallafin da take bawa kasar ta Gambia a shekara ta 2014 bayan da tsohon shugaban Kasar Yahyaha Jame wanda ya share shekaru 22 yana shugabancin kasar da kuma wasu abubuwan da kungiyar ta EU bata ji dadi ba.
Da wannan dalili da kuma wasu da dama ne. bayan faduwarsa a zaben ranar daya ga watan Decemba da ta gabata kasashen duniya musamman kasashen yammacin Afrika suka takurawa Yahyah Jame ya bar kujejera shugabancin kasar ya kuma shiga gudun hijira a kasar Equetorial Guinea.
Banda wannan tallafin dai, har ila yau ana saran sabuwar gwamnatin kasar ta Gambia za ta sami tallafin bankin duniya don farfado da tattalin arzikin kasar.288